Bangaren al'adu da fasaha:A ranar ashirin da shidda ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku
da tamanin da tara hijira shamsiya ne a huseiniyar Darbar Amir Khan da ke birnin Imruha na kasar Indiya aka gudanar da wani zaman taro na binciken irin hakkokin da mata suke da shi a Musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A ranar ashirin da shidda ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ne a huseiniyar Darbar Amir Khan da ke birnin Imruha na kasar Indiya aka gudanar da wani zaman taro na binciken irin hakkokin da mata suke da shi a Musulunci.Said Athar Abbas a lokacin day a gabatar da jawabinsa ya yi bayani dalla-dalla kan irin hakkokin da mata suke da shi a tsarin Musulunci kuma babu wani addini ko tsari day a kare da yin bayani kan hakkokin mata daidai da yanayinta da tsarinta kuma aiki da hakkokin mata kamar yadda Musulunci ya shata ko shakka babu zai inganta rayuwarsu ta zaman takewa da yancinta a tsakanin abukkan zamanta maza.
731700