IQNA

Shugaban Kwamitin Shi'a A Masar Bai Gamsu Da Yanayinsu A kasar Ba

14:50 - January 18, 2011
Lambar Labari: 2066916
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Al-duraini babban daraktan majalisar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, ya nuna rashin gamsuwarsa da yanayin da suke rayuwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alyaum Sabi ta kasar Masar cewa, muhammad Al-duraini babban daraktan majalisar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, ya nuna rashin gamsuwarsa da yanayin da suke rayuwa a kasar ta Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah a kasar suna daga cikin masu fuskantar danniya da nuna musu wariy a acikin lamurra da dama daga gwamnatin kasarsu, duk da cewa wannan matsala mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suna fiuskantar irin wannan matsala a kasashen larabawa da dama.

Hajj Muhammad Al-duraini babban daraktan majalisar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kasar Masar, ya nuna rashin gamsuwarsa da yanayin da suke rayuwa a kasar, sakamakon dane hakkokinsu da mahukunta suke yi.

732002



captcha