Bangaren kasa da kasa, An bude zaman taron kungiyar majalisun dokoki na kasashen musulmi a birnin Abu Dhabi fadar mulkin kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar shagabannin majalisu daga kasashen musulmi daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, an bude zaman taron kungiyar majalisun dokoki na kasashen musulmi a birnin Abu Dhabi fadar mulkin kasar hadaddiyar daular larabawa, tare da halartar shagabannin majalisu daga kasashen musulmi mambobi a kungiyar OIC.
Rahoton ya ci gaba da cewa zaman zai yi dubi kan muhimman batutuwa da ka gabatar a zaman kwamitin na baya, tare dakuma duba wasu daga cikin lamurran da suke ci ma kasashen musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan lokaci a duniya, tare da gabatar da shawarwari na matakan da ya kamata a dauka domin warware su.
Kimanin mutane 400 ne da suka hada da shugabannin majalisun dokokin kasashen musulmi da tawagoginsu suke halartar zaman taron, bugu da kari kuma ana sa ran daukar matakai na bai daya dangane da batun mamayar yankunan palalstinawa da Isra'ila ke yi.
732737