IQNA

Wani Malamin Jami'ar Hamburg A Kasar Jamus Ya Karbi Addinin Muslunci

16:37 - January 20, 2011
Lambar Labari: 2067892
Bangaren kasa da kasa, Wani daya daga cikin manyan malaman jami'ar Hamburg ta kasar Jamus ya karbi addinin muslunci, bayan day a kai wata ziyara a birnin Karbala mai alfarma, inda yanayin rayuwar musulmi da ayyukan ibadarsu ya yi babban tasiri a cikin zuciyarsa, a nan take ya karbi addinin muslunci, kuma zabi bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah.


Kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun an bayyana cewa, wani daya daga cikin manyan malaman jami'ar Hamburg ta kasar Jamus ya karbi addinin muslunci, bayan da ya kai wata ziyara a birnin Karbala mai alfarma, inda yanayin rayuwar musulmi da ayyukan ibadarsu ya yi babban tasiri a cikin zuciyarsa, a nan take ya karbi addinin muslunci, kuma zabi bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai Hard Shinadar ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na biyu day a ziyarci wannan birnin mai tsarki, kuma hakikanin gaskiya ya tasirantu matuka dangane da yadda mabiya tafarkin iyalan gidan manzon suke gudanar lamurransu na addini.

Musuluntar daya daga cikin manyan malaman jami'ar Hamburg ta kasar Jamus, bayan da ya kai wata ziyara a birnin Karbala mai alfarma, inda yanayin rayuwar musulmi da ayyukan ibadarsu ya yi babban tasiri a cikin zuciyarsa, babban lamari ne a cikin tarihin harkar jami'a akasar Jamus.

733515




captcha