IQNA

Kasashen Yamamcin Turai Na Hankoron Saka Sabani Tsakanin Musulmi

16:36 - January 20, 2011
Lambar Labari: 2067898
Bangaren siyasa, Wasu daga cikin kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun saka sabani da rashin fahimtar juna tsakanin kasashen musulmi, ta yadda za su wargaza duk wata fahimtar juna tsakaninsu, musamman ma kan batutuwa da suka shafi banbancin mazhaba.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizokhane millat an bayyana cewa, a zaman tattaunawar da ya gudana tsakanin shugabannin majalisun dokokin kasashen musulmia birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya yi wa masu halartar taron hannunka mai sanda da cewa, wasu daga cikin kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun saka sabani da rashin fahimtar juna tsakanin kasashen musulmi, ta yadda za su wargaza duk wata fahimtar juna tsakaninsu, musamman ma kan batutuwa da suka shafi banbancin mazhaba tsakanin mabiya addinin mulunci.

Ya ce dole ne musulmi su zama cikin fadaka dangane da abin da ake kulla musu na makirci daga kasashen yammci, wadanda ba su fatan ganin duk wani ci gaba tsakanin kasashen muslmi baki daya, kuma wannan shi ne abin da Iran take hankoron ganin an kawo karshen hakan.

733273

captcha