Bangaren kasa da kasa, Za abude wata cibiya ta tantance ayyukan nassosin kur’ani mai tsarki ta hanyar na’urorin digital, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta birnin Madina za ta dauki nauyin gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alhayat an bayyana cewa, za abude wata cibiya ta tantance ayyukan nassosin kur’ani mai tsarki ta hanyar na’urorin digital, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta birnin Madina za ta dauki nauyin gudanarwa a cikin ‘yan watannin da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan aiki na da matukar muhimmanci wajen tantance nassosi da aka saka a cikin na’urorin digital, domin kuwa duk abin aka riga aka saka acikin na’ura haka za ta karbe shi, idan kuma da kuskure a cikinsa haka za a ci gaba da karanta, wanda hakan yana tattare da hadari wajen yada manufofin kur’ani mai tsarki.
Bude cibiya ta tantance ayyukan nassosin kur’ani mai tsarki ta hanyar na’urorin digital, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta birnin Madina za ta dauki nauyin gudanarwa, zai bayar da dama wajen gudanar muhimman ayyuka na kur’ani da za su amfanar da masu koyon karatu da kuma nazari.
734224