Bangaren kasa da kasa, An yi Allawadai da ruda makabartun musulmi da yahuadawan sahyuniya suke yi a gabacin birnin Qods, da nufin mayar da wurin wajen ajiye kayan tarihin yahudawa a birnin mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa ya habarta cewa, an yi Allawadai da ruda makabartun musulmi da yahuadawan sahyuniya suke yi a gabacin birnin Qods, da nufin mayar da wurin wajen ajiye kayan tarihin yahudawa a birnin mai alfarma, da nufin tsokanar larabawa da mabiya addinin muuslunci.
Bayanin ya ci gab ada cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana daukar matakan tsokana tare neman rikici tsakaninta al’ummar palastinu, duk kuwa da irin Allawadai da take fuskanta daga al’ummomin duniya, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, inda ake kallon goyon bayan da take samu daga Amurka shi ne bababn abin da ke kara karfafa gwiwarta.
Yin Allawadai da rusa makabartun musulmi da yahuadawan sahyuniya suke yi a gabacin birnin Qods, da nufin mayar da wurin wajen ajiye kayan tarihin yahudawa a birnin mai alfarma, ya nuna matsayin al’ummomin duniya kan zalunci da danniyar yahudawan sahyuniya kan al’ummar palastinu.
734258