IQNA

An Nuna Wani Bugun Kur'ani A Yanar Gizo Da ya Kwashe Shekaru 500

10:14 - January 23, 2011
Lambar Labari: 2068971
Bangaren kasa da kasa, Kakakin jami'ar birnin Manchester na kasar Birtaniya ya bayyana cewa, an nuna wani dadadden kur'ani mai tsarki da aka rubuta tun kimanin shekaru dari biyar da suka gabata a cikin shafin yanar gizo na wannan jami'a.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-ilm ta kasar Morocco an bayyana cewa, Kakakin jami'ar birnin Manchester na kasar Birtaniya ya bayyana cewa, an nuna wani dadadden kur'ani mai tsarki da aka rubuta tun kimanin shekaru dari biyar da suka gabata a cikin shafin yanar gizo na jami'ar ta Manchester.

Ya ci gaba da cewa wannan kur'ani an rubuta shi ne da hannu, kuma takardun da aka yi amfani da su wajen rubutun sun tsofa sosai, a kan haka ne ma ba a jiye kurnin wurin da hannayen mutane za su iya kaiwa ba, domin kada wani bangarensa ya samu matsala saboda tsufa.


Kakakin jami'ar birnin Manchester na kasar Birtaniya ya bayyana cewa, an nuna wani dadadden kur'ani mai tsarki da aka rubuta tun kimanin shekaru dari biyar da suka gabata a cikin shafin yanar gizo na wannan jami'a wadda daya ce daga cikin dadaddun jami'oi na duniya.

734491




captcha