IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Tunawa Da Cika Kwanaki Arba'in Na Shahadar Imam Hussain (AS)

15:01 - January 24, 2011
Lambar Labari: 2069519
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma sahabbansa da suke tare da shi a ranar Ashura, wanda za a gudanar a birnin London na kasar Birtania.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jafariya News an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma sahabbansa da suke tare da shi a ranar Ashura, wanda za a gudanar a birnin London na kasar Birtania a ranar Talata idan Allah ya kaimu.

Rahoton ya ci gaba da cewa wannan taro wanda cibiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) ta kasar Birtaniya da ke babban ofishi a birnin London fadar mulkin kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, zai samu halar musulmi da dama, da suka hada da malamai da kuma masana musulmi daga sassa na kasar.

Daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar da laccoci, da kuma bayanai kan hakianin abin da ya faru da iyalan gidan manzon Allah a ranar Ashura, da kuma irin darussan da musulmi za su iya dauka daga sadaikantarwar Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzo (SAW) da kuma sahabban Imam da suka kasance tare da shi a ranar Ashura.

Gudanar da tarukan tunawa da cika kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) tare da iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma sahabbansa da suke tare da shi a ranar Ashura, wanda za a gudanar a birnin London na kasar Birtania, na matukar muhimmanci wajen kara fito da zalunci da aka yi wa iyalan manzon Allah (SAW).

735318
captcha