IQNA

Za A Bude Wata Cibiyar Nazarin Kur'ani A Shafin Yanar Gizo

19:57 - January 25, 2011
Lambar Labari: 2070196
Bangaren kasa da kasa, Za a bude wada cibiya da zata rika gudanar da ayyukanta ta hanyar yanar gizo domin yin nazari kan alkur'ani da kuma adana nau'oin rubutunsa, wanda cibiyar ayyukan bugun kur'ani ta sarki Fahad da ke birnin Madina ta dauki nauyin gudanarwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Gazette an bayyana cewa, za a bude wada cibiya da zata rika gudanar da ayyukanta ta hanyar yanar gizo domin yin nazari kan alkur'ani da kuma adana nau'oin rubutunsa, wanda cibiyar ayyukan bugun kur'ani ta sarki Fahad da ke birnin Madina ta dauki nauyin gudanarwa da nufin sawwaka masu bincike.

Bayanin ya ci gab ada cewa babban daraktan cibiyar Muhammad Aufi shi ne ya sanar da hakan, ya kara da cewa ko shakka babu cibiyar ta gunar da ayyuaka makamantan wannan, amma shi aikin samar da cibiya mai zaman kanta a yanar gizo domin gudanar da wannan gagarumin aiki, na tattare da muhimmanci na musamman.

Bude wada cibiya da zata rika gudanar da ayyukanta ta hanyar yanar gizo domin yin nazari kan alkur'ani da kuma adana nau'oin rubutunsa, wanda cibiyar ayyukan bugun kur'ani ta sarki Fahad da ke birnin Madina ta dauki nauyin gudanarwa, abban ci gaba ne ga harkar bincike kan ilmomin kur'ani mai tsarki.

735557



captcha