IQNA

An Gudanar Da Zaman Taro Mai Taken Ranar Imam Hussain (AS) A New York

19:57 - January 25, 2011
Lambar Labari: 2070197
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani zaman taro a birnin New York na kasar Amurka mai taken ranar Imam Hussain (AS) wanda ke da dangantaka da zagayowar ranar tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadarsa tare da iayalansa da sahabbansa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sijny an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin New York na kasar Amurka mai taken ranar Imam Hussain (AS) wanda ke da dangantaka da zagayowar ranar tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadarsa tare da iayalansa da sahabbansa a Karbala.

Babbar cibiyar musulmi mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke birnin New York ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro, wanda ya samu halartar daruruwan musulmi mabiya mazhabar shi'a da ma wasu 'yan sunna, domin raya wannan rana mai labarka ta cika kwanaki da shahadar Imam Hussain (AS)

Gudanar da wani zaman taro a birnin New York na kasar Amurka mai taken ranar Imam Hussain (AS) wanda ke da dangantaka da zagayowar ranar tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadarsa tare da iyalansa da sahabbansa a ranar Ashura.

735576



captcha