Bangaren kasa da kasa, Addinin muslunci addini ne na 'ya uwantaka, kaunar juna da afuwa da kyautata wa kowa, da sauran abubuwa da wannan addini ya kebanta da su da suka danganci 'yan adamtaka, wanda hakan ya sanya shi ya zama mafi jan hankali a tsakanin dukkanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantaw ada ta hada shi da daya daga cikin masu gudanar da nazari da bincike mai zurfi kan addinin Musulunci Artan Bisarak ya bayyana cewa, Addinin muslunci addini ne na 'ya uwantaka, kaunar juna da afuwa da kyautata wa kowa, da sauran abubuwa da wannan addini ya kebanta da su da suka danganci 'yan adamtaka, wanda hakan ya sanya shi ya zama mafi jan hankali a tsakanin dukkanin addinai da aka safkar daga sama da ma sauran addina na duniya baki daya.
Ya ci gaba da cewa addinin muslunci yana koyar da dan adam yanayin rayuwa ta zamantakewa, da kuma yadda zai taimaka wa mai rauni, da karfafa gwai ga masu aikata alhairi a cikin al'umma, ta yadda kyakkyawa zai zama abin koyi ga kowa.
Ko shakka babu addinin muslunci addini ne na 'ya uwantaka, kaunar juna da afuwa da kyautata wa kowa, da sauran abubuwa da wannan addini ya kebanta da su da suka danganci 'yan adamtaka.
735602