IQNA

An Buga Tare Yada Wata Nashara Mai Suna Palastinu Musulma

18:17 - January 26, 2011
Lambar Labari: 2070864
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada wata nashara mai suna palastinu musuulma a cikin harshen larabci a cikin shekara ta 2011, wadda ofishin kungiyar gwagwarmayar musulnci ta Hamas a birnin Tehran ya dauki nauyin bugawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an buga tare da yada wata nashara mai suna palastinu musuulma a cikin harshen larabci a cikin shekara ta 2011, wadda ofishin kungiyar gwagwarmayar musulnci ta Hamas a birnin Tehran ya dauki nauyin bugawa, domin kara fito da matsayin palastinawa ‘yan gwagwarmaya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan nashara ta yi karin haske kan yadda tattaunawa tsakanin palastinawa da kuma yahudawan sahyuniya ta ci tura, sakamakon irin matakan banzatarwa da haramtacciyar kasar Isra’ila take dauka kan masu gudanarwa da tattaunawa tare da ita, sakamakon irin goyon bayan da take samu daga uwar gijiyarta.
Buga tare da yada wata nashara mai suna palastinu musuulma a cikin harshen larabci a cikin shekara ta 2011, wadda ofishin kungiyar gwagwarmayar musulnci ta Hamas a birnin Tehran ya dauki nauyin bugawa, na da matukar muhimmanci wajen kara fito da matsayin kungiyoyin gwagwarmaya kan attaunawa da ake yi da yahudawa.
735535



captcha