IQNA

Allah Ya Yi Wa Ayatollah Sheikh Muhammad Ali Al-Umari Rasuwa

18:16 - January 26, 2011
Lambar Labari: 2070865
Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi wa babban malamin addinin musulunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya rasuwa, wanda ya taka gagarumar rawa wajen yada tunanin gidan manzon Allah a cikin kasar wadda ta kasance daya daga cikin kasashen larabawa da ake danne hakkokin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid an bayyana cewa, Allah ya yi wa babban malamin addinin musulunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya rasuwa, wanda ya taka gagarumar rawa wajen yada tunanin gidan manzon Allah a cikin kasar wadda ta kasance daya daga cikin kasashen larabawa da ake danne hakkokin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da karfin tuwo.
Babban malamin dai ya yi fama da rashin lafiya a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ya kwashe tsawon kwanaki kwance a asibiti a birnin Madina mai alfarma, a jiya kuma rai ya yi halinsa. An haifi wannan bawan Allah a cikin shekara ta 1911, kuma ya kwashe tsawon shekaru kimanin sattin yana isar da sakon iyalan gidan manzon Allah ga al’ummar Hijaz, duk kuwa da irin kuncin da ya fuskanta daga mahukunta wahabiyawan Saudiyya.
Rasuwar wannan babban malamin addinin musulunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya, wanda ya taka gagarumar rawa wajen yada tunanin gidan manzon Allah a cikin kasar wadda ta kasance daya daga cikin kasashen larabawa da ake danne hakkokin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo, babban rashi ga duniya mazhabar iyalan gidan manzo.

736267
captcha