IQNA

Ana Shirin Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Qatar

18:15 - January 26, 2011
Lambar Labari: 2070866
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fara mulkin kasar Qatar, wadda ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na goma sha takwas.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na muhit an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fara mulkin kasar Qatar, wadda ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na goma sha takwas a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa gasar ta zata shafi dukkanin bangarori na harda, da kuma karatu gami dokokin karatu wato tajwidi, inda za a kasa mahalarta gasa zuwa kashe daban-daban, daidai da abin suka zaba a cikin gasar, wasu za su gudanar da harda ne daga farkon kur’ani zuwa rubu’i, wasu kumazuwa rabinsa, yayain da wasu za su harda da karatu na kur’ani baki daya.
Ana ci gaba da yin rijistar sunaye duk a cikin shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fara mulkin kasar Qatar, wadda ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na goma sha takwas kasar ta Qatar. 736197

captcha