IQNA

Za A Gudanar Da Taro Mai Taken Imam Hussain (AS) Da Kur’ani A Saudiyya

18:17 - January 26, 2011
Lambar Labari: 2070867
Bangaren kasa da kasa, Za agudanar da wani zaman taro mai taken Imam Hussain (AS) da kur’ani mai tsarki, wanda za a gudanar a karo na biyu a garin Aujam dake cikin lardin Katif a kasar Saudiyya, wanda zai mayar da hankali kan matsayin Imam Hussain (AS) ta fuskacin yada koyarwar kur’ani a cikin dukkanin ayyukansa a cikin rayuwar zamantakewa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na Muzn cewa, Za agudanar da wani zaman taro mai taken Imam Hussain (AS) da kur’ani mai tsarki, wanda za a gudanar a karo na biyu a garin Aujam dake cikin lardin Katif a kasar Saudiyya, wanda zai mayar da hankali kan matsayin Imam Hussain (AS) ta fuskacin yada koyarwar kur’ani a cikin dukkanin ayyukansa a cikin rayuwar zamantakewa, da kuma yadda yakasance babban misali wajen aikata koyarwar kur’ani mai tsarki.
A bangare guda kuma bayanin ya yi ishara da cewa Allah ya yi wa babban malamin addinin musulunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya rasuwa, wanda ya taka gagarumar rawa wajen yada tunanin gidan manzon Allah a cikin kasar wadda ta kasance daya daga cikin kasashen larabawa da ake danne hakkokin mabiya tafarkin iyalan gidan manzo (SAW).
Rasuwar wannan babban malamin addinin musulunci kuma jagoran mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya, wanda ya taka gagarumar rawa wajen yada tunanin gidan manzon Allah a cikin kasar Saudiyya babban abin alhini ga musulmi baki daya. 736234
captcha