IQNA

Kasashen Iran Da Qatar Da Kara Fadda Danganta Ta Fukskar Al’adun Musulunci

Bangaren al’adu, Shugaban cibiyar bunkasa harkokin al’dun musulunci na kasar Iran Muhammad Bakir Khoramshad ya bayyana cewa, kasashen Iran da Qatar suna taka gagarumar rawa wajen bunkasa harkokin al’dun addinin musulunci duniyar musulmi ta yau.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a da manema labarai na cibiyar bunkasa harkokinal’adu an bayyana cewa, Shugaban cibiyar bunkasa harkokin al’dun musulunci na kasar Iran Muhammad Bakir Khoramshad ya bayyana cewa, kasashen Iran da Qatar suna taka gagarumar rawa wajen bunkasa harkokin al’dun addinin musulunci duniyar musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa a bangare guda kuma ana shirin fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Doha fara mulkin kasar Qatar, wadda ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karo na goma sha takwas, yanzu haka dai ana ci gab ada yin rijistar sunayen masu bukatar shiga gasar har zuwa makonni biyu masu zuwa.
Wannan gasar ta zata shafi dukkanin bangarori na harda, da kuma karatu gami dokokin karatu wato tajwidi, inda za a kasa mahalarta gasa zuwa kashe daban-daban, daidai da abin suka zaba a cikin gasar, wasu za su gudanar da harda ne daga farkon kur’ani zuwa rubu’i, wasu kumazuwa rabinsa, yayain da wasu za su harda da karatu kur’ani daga farkonsa har karshe.
736199