Bangaren siyasa da zamantakewa, Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi ga mahalarta taron tunawa da cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a garin Ba’alabak da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad an bayyan acewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi ga mahalarta taron tunawa da cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a garin Ba’alabak da ke kudancin kasar ta Lebanon.
Bayanin ya ci gaba da cewa jawabin na Sayyid Nasrullah zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka danganci yanayin da kasar take ciki ta fuskacin siyasa, musamman ma tun bayan kifar da gwamnatin Sa’ad Hariri a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya baiwa bangaren adawa ya iya kafa sabuwar ggwamnati, da ake sa ran za a yi nan ba da jimawa ba.
Babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabin ne ga mahalarta taron tunawa da cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a garin Ba’alabak da ke kudancin kasar, kasantuwarsu mabiya mazhabar iyalan gidan manzo kuma bangaren adawa.
736209