IQNA

‘Yan Sunna Sun Halarci Taron Ranar Arba’in Ta Imam Hussain (AS) A Istanbul

Bangaren al'adu da fasaha, Dubban mabiya tafarkin sunna ne suka halarci taron cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura, wanda aka gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) ta kasar Turkiya an bayyana cewa, dubban mabiya tafarkin sunna ne suka halarci taron cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura, wanda aka gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Turkiya na daya daga cikin kasashen musulmi da suke taka gagarumar rawa a cikin harkokin musulmi na duniya, musamman lamurran da suka danganci yankin gabas ta tsakiya, wanda ga dukkanin alamu hakan na samun karbuwa daga al’ummar kasar wadanda akasarinsu musulmi ne mabiya tafarkin sunna, amma a cikin ‘yan lokutan nan ana samun fahimtar mazhabar iyalan gidan manzo.
Dubban mabiya tafarkin sunna ne suka halarci taron cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a ranar Ashura, wanda aka gudanar a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya.
735981