IQNA

Gwamnatin Yahudawan Sahyuniya Na Hankoron Yahudantar Da Qods

12:55 - January 27, 2011
Lambar Labari: 2071040
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin yahudawan sahyuniya ta haramtacciyar kasar Isara'ila na hankoron yahudantar da birnin Qods mai alfarma, a kan haka ne ma babban sakataren cibiyar bunkasa ilimi da ala'adun kasashen musulmi ya kira wani zaman taro na gaggawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta haramtacciyar kasar Isara'ila na hankoron yahudantar da birnin Qods mai alfarma, a kan haka ne ma babban sakataren cibiyar bunkasa ilimi da ala'adun kasashen musulmi ya kira wani zaman taro na gaggawa tsakanin kasashen musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa Abdulaziz Tuwaijari ya jaddada muhimmancin cewa dole dukkanin kasashen musulmi su dauki matakai na bai daya domin takawa yahudawan sahyuniya birki kan tabargazar da suke tafkawa kan wurare masu tsarki da ke cikin birnin Qods.

Gwamnatin yahudawan sahyuniya ta haramtacciyar kasar Isara'ila na hankoron yahudantar da birnin Qods mai alfarma, a kan haka ne ma babban sakataren cibiyar bunkasa ilimi da ala'adun kasashen musulmi ya kira wani zaman taro na musulmi.

736729

captcha