Bangaren kasa da kasa, Babban malamin addinin Musulunci na kasar Saudiyya kuma jagora daga cikin jagororin mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah a kasar marigayi Ayatollah Muhammad Ali Al-umari, ya kebantu da siffofin imani da takawa da zurfin ilimi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tasahr rasid cewa, babban malamin addinin Musulunci na kasar Saudiyya kuma jagora daga cikin jagororin mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah a kasar marigayi Ayatollah Muhammad Ali Al-umari, ya kebantu da siffofin imani da takawa da zurfin ilimi a lokacin rayuwarsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wata zantawa da ta hada wakilin kamafanin dillancin labaran iqna da daya daga cikin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Saudiyya ali Alhabib, ya bayyana cewa hakika rasuwa babban malami kamar sheikh Alumari rashi ga dukkanin duniyar musulmi baki daya.
Malamin ya rayu kimanin shekaru dari daya a duniya, ya kuma taka gagarumar rawa wajen yada ilmomin addinin musamman ma koyarawar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi.
736808