IQNA

Za A Gudanar Da Taro Mai Take Juyin Musuluncin Iran A Birnin London

13:08 - January 27, 2011
Lambar Labari: 2071042
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro mai take juyin juya halin Musulunci a Iran a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, a lokacin gudanar da bukukuwan cika shekaru 32 da samun nasar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el cewa, Za a gudanar da wani zaman taro mai take juyin juya halin Musulunci a Iran a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, a lokacin gudanar da bukukuwan cika shekaru 32 da samun nasar juyin juya halin Musulunci a kasar, bayan da aka kifar da sarki shah mai kawance da Amurka da yahudawan sahyuniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin Musulunci ta birnin London za ta dauki nauyin shirayawa da gudanarwa, zai yi dubi ne kan muhimman batutuwa da suka danganci irin nasarorin da juyin ya samu cikin shekaru talatin da biyu da girkuwarsa.

Gudanar da wani zaman taro mai take juyin juya halin Musulunci a Iran a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, a lokacin gudanar da bukukuwan cika shekaru 32 da samun nasar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, na nuni da irin karbuwa da juyin ke samu.

736655
captcha