Bangaren siyasa da zamantakewa: shugaban ofishin musulmin Kafkaz ya ki ganawa da malaman addini masu adawa da dokar hana sanya hijabi a jamhuriyar Azarbaijan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugaban ofishin musulmin Kafkaz ya ki ganawa da malaman addini masu adawa da dokar hana sanya hijabi a jamhuriyar Azarbaijan.Taron gangami na masu adawa da dokar hana sanya hijabi a kasar Azarbaijan sun kaisu saba'in daga shugabannin musulmin kasar a birnin Baku kuma wadanda suka halarci wannan taron gangamin sun kwashe sa'o'I biyar a masallacin Taze bir inda suka bayyana matsayinsu a fili karara da adawarsu kan wannan dokar da lahanin da ke tattare da ita.
736406