IQNA

An Rufe Gawar Ayatollah Muhamamd Al-umari A makabartar Baki Da Ke Madina

18:51 - January 29, 2011
Lambar Labari: 2072020
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da janazar babban mamalimanin addinin Musulunci kuma jagoran mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah (SAW) a kasar saudiyya Ayatollah Muhammad Ali Al'umari, inda aka rufe gawarsa a makabartar nan mai daraja ta Baki da ke birnin Madina.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, an gudanar da janazar babban mamalimanin addinin Musulunci kuma jagoran mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah (SAW) a kasar saudiyya Ayatollah Muhammad Ali Al'umari, inda aka rufe gawarsa a makabartar nan mai daraja ta Baki da ke birnin Madina mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan janaza ta babban malami bawan Allah ta samu halarta dubun dubatar mabiya tafarkin manzon Allah a kasar saudiyya, ya dai rasu ne bayan fama da rashin lafiya inda aka kwantar da shi a wani asibiti da ke birnin na Madina.

An gudanar da janazar babban mamalimanin addinin Musulunci kuma jagoran mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah (SAW) a kasar saudiyya Ayatollah Muhammad Ali Al'umari, inda aka rufe gawarsa a makabartar nan mai daraja ta Baki da ke birnin.

737550





captcha