IQNA

Wasu Yahudawan Sahyuniya Suna Yin Tozarta Kur’ani Mai Tsarki

17:02 - January 30, 2011
Lambar Labari: 2072671
Bangaren kasa da kasa, Wani wurin sayar da abinci mallakin yahudawan sahyuniya a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, ya buga wani abin goge hannu da aka rubuta ayar kur’ani mai tsarki a kansa, da nufin yin tozarci ga addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na al’arab an bayyana cewa, wani wurin sayar da abinci mallakin yahudawan sahyuniya a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, ya buga wani abin goge hannu da aka rubuta ayar kur’ani mai tsarki a kansa, da nufin yin tozarci ga addinin musulunci da kuma tsokanar musulmi.
Wannan dakin cin abinci da ke garin Telaviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila, ya saka wannan abin goge hannu domin a yi amfani da shi da kuma goge teburan da yahudawa suka ci abinci, kuma bayan an gama ana sakawa acikin kwandon shara da ke cikin dakin cin abincin.
Rahoton ya tabbatar da cewa dukkanin ayoyin an dauko su ne daga cikin surat Muhammad (SAW) wadnada suke yin magana kan jihadi a tafarkin Allah, wannan dai ba shi ne karon farko da yahudawan sahyuniya suke yin irin wannan danyen aiki ba.
A kwanakin baya wasu yahudawan sahyuniya sun kai hari masallacin garin Nablus da ke gabar yamma dakogin Jordan, inda suka tozarta kur’ani mai tsarki tare da cinna ma masallacin wuta baki daya.
738016


captcha