IQNA

Alkalan Gasar Kur’ani Su Yi La’akari Banbanci Larabawa Da Wadanda Ba Su Ba

17:03 - January 30, 2011
Lambar Labari: 2072672
Bangaren kasa da kasa, Masu halartar gasar kur’ani da asalin harshensu ba larabci ne sun fi fitar da haruffan kur’ani mai tsarki kamar yadda ya kamata a kan masu karatu larabawa, wanda dole ne masu kula da alkalancin gasar karatun kur’ani su yi la’akari da hakan, kuma su bayar da maki gare su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da hada wakilinsa da fitaccen marancin kur’anin nan dan kasar Syria Ridawan Darwish ya bayyana cewa, masu halartar gasar kur’ani da asalin harshensu ba larabci ne sun fi fitar da haruffan kur’ani mai tsarki kamar yadda ya kamata a kan masu karatu larabawa, wanda dole ne masu kula da alkalancin gasar karatun kur’ani su yi la’akari da hakan, kuma su bayar da maki gare su kan wannan kokari.
Ya ci gaba da cewa larabawa suna furuci da da haruffan larabci ne daidai da yadda suke yin magana, duk da cewa makaranta suna kokarin su kiyaye hakan a cikin karatun kur’ani mai tsarki, wanda shi yana da hanyoyinsa na musamman da ake karanta sabanin yadda ake yin magana ta yau da kullmu.
Ya ce wadanda larabci ba shi ne harshensu ba, suna koyon kur’ani tun daga farko a kan yadda ake karanta shi, saboda haka babu wani abin zai kawo ma lahanin sautinsu mushkila, a kan haka a mafi yawan lokuta suna fin larabawa iya karatun kur’ani da fitar da sauti yadda ya kamata.
A kan haka sau da yawa masu halartar gasar kur’ani da asalin harshensu ba larabci ne sun fi fitar da haruffan kur’ani mai tsarki kamar yadda ya kamata a kan masu karatu larabawa, wanda dole ne masu kula da alkalancin gasar karatun kur’ani su yi la’akari da hakan.
737927




captcha