Bangaren al’adu da fasaha, An bayyana irin muhimmancin rawar da mata suka taka a lokacin yunkurin juyin juya halin musulunci a kasar Iran, wanda ya kai ga kawo karshen mulkin kama karya na sarki Shah, tare da maye gurbinsa da mulki da ya ginu kan yardar jama’a da zabinsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani bayani da ya nakalto da bangaren hulda da jama’a na cibiyar bunkasa harkokin al’adu ta Irwan an bayyan acewa, an yaba da irin muhimmancin rawar da mata suka taka a lokacin yunkurin juyin juya halin musulunci a kasar Iran, wanda ya kai ga kawo karshen mulkin kama karya na sarki Shah, tare da maye gurbinsa da mulki da ya ginu kan yardar jama’a da zabinsu ba tare da wani tilasci a cikin hakan ba.
An yi wannan bayani ne a lokacin da ake gudanar da wani zama na basi kan harkokin ilmi da kuma matsayin juyin juya halai wajen habbaka harkokin ilmi a jamhuriyar musulunci, wadda ya kawo gagarumin ci gaba da wannan fuska a cikin shekaru talatin biyu.
Muhimmancin rawar da mata suka taka a lokacin yunkurin juyin juya halin musulunci a kasar Iran, wanda ya kai ga kawo karshen mulkin kama karya na sarki Shah, tare da maye gurbinsa da mulki da ya ginu kan yardar jama’a da zabinsu shi ne sirrin nasar.
737597