Bangaren kasa da kasa, An nuna wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta kan addinin muslunci a wani taro da aka gudanar birnin Paris fadar mulkin kasar faransa, da ke bahasi kan muhimman Musulunci da kuma rawar da ya taka ta fuskacin bunkasa al'adun dan adam.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews cewa, an nuna wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta kan addinin muslunci a wani taro da aka gudanar birnin Paris fadar mulkin kasar faransa, da ke bahasi kan muhimman Musulunci da kuma rawar da ya taka ta fuskacin bunkasa al'adun dan adam a tsawon tarihi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin jami'an na birnin paris din suka shirya gudanar da wannan zaman taron, domin bayar da muhimmanci ga irin rawar da wannan addini ya taka ta fuskoki da dama domin bunkasa ci gaban dan adam, wanda tarihinsa ba zai taba mantawa da hakan ba.
Nuna wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta kan addinin muslunci a wani taro da aka gudanar birnin Paris fadar mulkin kasar faransa, da ke bahasi kan muhimman Musulunci da kuma rawar da ya taka ta fuskacin bunkasa al'adun dan adam, na da gagarumin muhimmanci ga musulmi.
738659