Bangaren siyasa da zamantakewa, Wasu daga cikin wakilan kwamitoci da kungiyoyin palastinawa mazauna kasar Spain sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta, sun yi wannan kira ne a cikin wata wasika da suka aikewa pira ministan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo daga Spain an bayyana cewa, wasu daga cikin wakilan kwamitoci da kungiyoyin palastinawa mazauna kasar Spain sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta, sun yi wannan kira ne a cikin wata wasika da suka aikewa pira ministan kasar ta Spain.
Bayanin ya ci gaba da cewa dubban palastinawa da suke zaune a kasar ne da suka hada wadanda suke da takardun zama cikakkun 'yan kasa da kuma wadanda suke gudun hijira ne suka rattaba hannu kan wannan takarda da akaewa pira ministan kasar ta Spain, da suke neman ya bi sahun sauran kasashen a suka amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Wasu daga cikin wakilan kwamitoci da kungiyoyin palastinawa mazauna kasar Spain sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta, sun yi wannan kira ne a cikin wata wasika da suka aikewa pira ministan kasar.
738283