IQNA

Tawagar Iran Za Ta Halarci Taron Makon Halal Da Aka Gudanar A Malazia

18:38 - January 31, 2011
Lambar Labari: 2073491
Bangaren siyasa da zamantakewa, Tawagar 'yan kasuwar Iran na shirin halartar tarn da za agudanar nan da watanni biyu masu zuwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia kan abincin halal, da zai samu halartar kamfanonin kasashen duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar 'yan kasuwan gabacin nahiyar Asia an bayyana cewa, tawagar 'yan kasuwar Iran na shirin halartar tarn da za agudanar nan da watanni biyu masu zuwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia kan abincin halal, da zai samu halartar kamfanonin kasashen duniya, musamman ma kasashen musulmi.

Rahoton ya ce kamfanonin Iran da dama sun nuna sha'awarsu ta halartar wannan taro da za a gudanar a mataki na kasa da kasa, musamman kamfanonin da suke samar da kayayyakin abinci na kasashen musulmi, bisa la'akari da cewa taro na abincin halal ga mabiya addinin Musulunci, wanda kuma kamfanonin kasashen musulmi ne suka fi sanin abin da za su samar na abincin halal.

Tawagar 'yan kasuwar Iran na shirin halartar tarn da za agudanar nan da watanni biyu masu zuwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia kan abincin halal, da zai samu halartar kamfanonin kasashen duniya daban-daban.

737998








captcha