Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wata babbar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa a Afirka ta kudu, wadda za ta kebanci dalibai 'yan makarantun sakandare a farkon wata mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Times Alive an habarta cewa, za a gudanar da wata babbar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa a Afirka ta kudu, wadda za ta kebanci dalibai 'yan makarantun sakandare a farkon wata mai zuwa a birnin Pritoria fadar mulkin kasar.
Gasar karatun kur'anin za a gudanar da ita ne a mataki na share fage, kuma za ta samu halartar daruruwan daliban makarantun sakandare na daga sassa daban-daban na kasar, wadanda za su taka gagarumar rawa wajen bayyan amatsayin musulmi masu karatu da hardar kur'ani a kasar Afirka ta kudu, wadda akasarin mazauna cikinta mabiya addinin kirista ne.
Bayanin ya kara da cewa za a gudanar da wata babbar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa a Afirka ta kudu, wadda za ta kebanci dalibai 'yan makarantun sakandare a farkon wata mai zuwa idan Allah ya kaimu.
738728