IQNA

An Fara Gudanar Da Horo Kan Farisanci A Suriya

Bangaren al'adu da fasaha:a karo na sha takwas an bude ajijiwan koyar da harshen farisanci a cibiyoyi na koyar da yaren a Lazkiya da ke karkashin ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Suriya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; a karo na sha takwas an bude ajijiwan koyar da harshen farisanci a cibiyoyi na koyar da yaren a Lazkiya da ke karkashin ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Suriya.A lokacin fara wannan horo Muhsin Takwa da ke ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin wani jawabi day a gabatar ga wadanda suka kammala karbar wannan horo a zangon day a gabata ya yi masu nuni da yadda harshen farisanci ke taka rawar gani wajen yada ilimi na addinin Musulunci.


739372