IQNA

Ministan Cikin Gida Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hijabi A Azarbaijan

Bangaren siyasa da zamantakewa: ministan cikin gida na kasar Azarbaijan ya bayyana matsayinsa kan sanya hijabi a wannan kasar ya jaddada cewa; mata sunada zabin irin kayan da za su sanya kuma babu wani hani kan abin da za su sanya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa; ministan cikin gida na kasar Azarbaijan ya bayyana matsayinsa kan sanya hijabi a wannan kasar ya jaddada cewa; mata sunada zabin irin kayan da za su sanya kuma babu wani hani kan abin da za su sanya.Ramil Uzub uf ya kara da bayyana cewa; Azarbaijan kasa ce mai yanci kan lamuran akida sabanin wasu kungiyoyi da ke bukatar a hana sanya hijabi a makarantun kasar.

739779