Bangaren kasa da kasa, Gidan talabijin din Aljazeera da ke watsa shirinsa kan tauraron dan adam daga kasar Qatar ya bada rahoton cewa, kashi casa’in da tara cikin dari na kwafi-kwafin kur’ani mai tsarki ake bugawa akasar Indonesia na da kuskure a cikin bugunsu, sakamakon buga su wata cibiya da ba ta musulmi ke yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, gidan talabijin din Aljazeera da ke watsa shirinsa kan tauraron dan adam daga kasar Qatar ya bada rahoton cewa, kashi casa’in da tara cikin dari na kwafi-kwafin kur’ani mai tsarki ake bugawa akasar Indonesia na da kuskure a cikin bugunsu, sakamakon buga su wata cibiya da ba ta musulmi ke yi a mtsayin kwangila da wasu cibiyoyin musulunci ko ‘yan kasuwa ke bayarwa ko masu kudi musulmi.
Wani shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Indonesia mai suna Alwafd ya naklato daga daraktan daya daga cikin cibiyoyin da ke buga kur’ani mai tsarki a kasar cewa, babbar matsalar da ake fuskanta ita ce, a lokacin da aka buga kur’ani akwai bukatar sake yin dubi a kan dukkanin abin da aka buga kafin yin kwafi-kwafi, amma abin takaici yadda aka yi bugun farko na samfuri ba tare da yin dubi sosai ba sai buga a hakan a kai kasuwa.
Talabijin din Aljazeera da ke watsa shirinsa kan tauraron dan adam daga kasar Qatar ya bada rahoton cewa, kashi casa’in da tara cikin dari na kwafi-kwafin kur’ani mai tsarki ake bugawa akasar Indonesia na da kuskure a cikin bugunsu, sakamakon buga su da wata cibiya da ba ta musulmi ke yi wata kila bisa kuskure ko da gangan.
739638