IQNA

Za A Bude Wata Cibiyar Kur’ani Mai Suna Alwaqayan A kasar Kuwait

14:30 - February 01, 2011
Lambar Labari: 2074106
Bangaren kasa da kasa, Abdullah Albarak shugaban cibiyar kula da nazarin addinin muslunci a karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Kuwait, ya bayyana cewa za a bude wata cibiyar nazari kan ayyukan musulunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-rayi ta kasar Kuwait cewa, kwamitin da ke kula da ayyukan shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Kuwait ya gabatar da shawar mayar da da gasar karatun kur’ani ta kasar da ake gudanarwa a kowace shekara a matsayin gasa ta kasa da kasa, za ta rika samun halartar makaranta da mahardata kur’ani daga sassa duniya na larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin shirya gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na kasar Kuwait ya gabatar wannan shawara ne bisa la’akari da yadda wannan gasa take samun karbuwa daga masu halartar ta, da kuma irin rawar da gwamnatin kasar take takawa wajen taimakama kwamitin wajen shiryata.
kwamitin da ke kula da ayyukan shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Kuwait ya gabatar da shawar mayar da da gasar karatun kur’ani ta kasar da ake gudanarwa a kowace shekara a matsayin gasa ta kasa da kasa, za ta rika samun halartar makaranta da mahardata kur’ani daga sassa duniya.
739381


captcha