Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin yahudawan sahyuniya ta amince da wani shiri na mamaye wani masallaci mallakin musulmi mazauna garin Haifa da ke arewacin yankin palastinu da yahudawa 'yan kaka gida suka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine info an bayyana cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta amince da wani shiri na mamaye wani masallaci mallakin musulmi mazauna garin Haifa da ke arewacin yankin palastinu da yahudawa 'yan kaka gida suka mamaye tun lokacin kafa harmtacciyar kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman hukumar yahudawan sahyuniya ta dauki wannan mataki ne saboda nuna wa palastinawa cewa ita ce da iko da su da kuma dukkanin abubuwan da suke komawa zuwa gare su, da kuma abubuwan da suka mallaka na ibada da na tarihi da dai sauransu.
Gwamnatin yahudawan sahyuniya ta haramtacciyar kasar Isra'ila ta amince da wani shiri na mamaye wani masallaci mallakin musulmi mazauna garin Haifa da ke arewacin yankin palastinu da yahudawa 'yan kaka gida suka mamaye.
740413