Bangaren kasa da kasa, Sayyid Lashin Bin Abul-farah shi ne ake yi wa lakabi da sheikhul kurra na birnin Madina mai alfarma, wanda dan asalin kasar Masar ne amma mazaunin kasar Saudiyya, wanda kuma Allah ya yi masa rasuwa a jiya litini, an kuma gudanar da janazarsa a birnin na Madina mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almadina ta kasar saudiyya an bayyana cewa, sayyid Lashin Bin Abul-farah shi ne ake yi wa lakabi da sheikhul kurra na birnin Madina mai alfarma, wanda dan asalin kasar Masar ne amma mazaunin kasar Saudiyya, wanda kuma Allah ya yi masa rasuwa a jiya litini, an kuma gudanar da janazarsa a birnin na Madina.
Bayanin ya ci gaba da cewa shehin malamin wanda ya bar duniya yana da shekaru 63, ya kwashe tsawon shekaru yana koyar da ilmomin kur'ani da kuma karatun kur'ani mai tsarki a babban masallacin manzon Allah (SAW) da ke birnin na Madina, inda yake dubban dalibai da suka yi karatu a hannunsa.
Sayyid Lashin Bin Abul-farah shi ne ake yi wa lakabi da sheikhul kurra na birnin Madina mai alfarma, wanda dan asalin kasar Masar ne amma mazaunin kasar Saudiyya, wanda kuma Allah ya yi masa rasuwa a jiya litini, an kuma gudanar da janazarsa a birnin na Madina mai alfarma.
740305