Bangaren kasa da kasa, Birnin Karbala mai alfarma ya shiga cikin manyan biranan duniya da suke samu ziyara daga miliyoyin mutane daga sassa na duniya, bayan da lamarin ziyarar wurare masu tsarki da ke cikin birnin ke ta kara samun bunkasa.
Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN an bayyana cewa, birnin Karbala mai alfarma ya shiga cikin manyan biranan duniya da suke samu ziyara daga miliyoyin mutane daga sassa na duniya, bayan da lamarin ziyarar wurare masu tsarki da ke cikin birnin ke ta kara samun bunkasa a kowane lokaci, musamman a cikin shekarun baya-bayan nan.
Babban jami'i mai kula da ayyukan kwamitin adana kayan tarihi da yawon shatawa na lardin Karbala Iftikhar Abbas shi ne ya sheda hakan, inda ya tabbatar da cewa ziyarar da ake kaiwa a birnin Karbala a kowace shekara da miliyoyin mutane ce masu yawa, wanda hakan ya mayar da birnin cikin manyan biranan da ke samun masu ziyara na duniya.
Akwai wurare masu tsarki a cikin birnin Karbala mai alfarma da suka hada hubbarorin iayalan gidan manzon Allah (SAW) wanda hakan ne sanya ya shiga cikin manyan biranan duniya da suke samu ziyara daga miliyoyin mutane daga sassa na duniya, bayan da lamarin ziyarar wurare masu tsarki da ke cikin birnin ke samun ci gaba.
740231