IQNA

An Gudanar Da Taron Girmama Mahardata Kur’ani Mai Tsarki A Palastine

16:25 - February 03, 2011
Lambar Labari: 2074680
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na girmama mahardata kur’ani mata palastinawa a yankin salafiyat da ke gabar yamma da kogin Jordan, da nufin kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da kiyaye hardarsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ma’a an bayyan acewa, an gudanar da wani zaman taro na girmama mahardata kur’ani mata palastinawa a yankin salafiyat da ke gabar yamma da kogin Jordan, da nufin kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da kiyaye hardarsu da kuma zaburar da masu bukatar shiga cikin harkar hardar kur’ani a yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a wannan taron an girmama mata arba’in da uku 43 da suka shiga cikin gasar hardar kur’ani da kuma ilmin tajwidi da aka gudanar a kwanakin baya, dagacin yankin salafiyat Abdulsattar Awwad ya gabatar da jawabi a wurin taron, inda ya bayyana cewa hakika mahardatan sun taka gagarumar rawa a lokacin gudanar da gasar.
Ya ce hakika sun canci gudiya ta musamman daga dukkanin al’ummar palastinu, ya kara da cewa yanzu haka dai an bude cibiyoyi da dama a yankin da nufin kara fadada ayyukan hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin al’ummar palastinu.
740752



captcha