Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da zaman makokin tunawa da ranar wafatin manzon Allah (SAW) a jahar California ta kasar Amurka, wanda cibiyar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke jahar za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saba-igc an bayyana cewa, za a gudanar da zaman makokin tunawa da ranar wafatin manzon Allah (SAW) a jahar California ta kasar Amurka, wanda cibiyar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke jahar za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a yau.
Rahoton ya ce za a fara gudanar da taron bayan kammala sallolin magariba da isha’i, daga nan kuma masu gabatar da jawabai za su fara, inda za ayi laccoci kan tarihin manzon Allah (SAW) da kuma gwagwarmayarsa a wajen isar da sakon madaukakakin sarki, da kuma abubuwan da ya hadu da su a lokacin safke wannan nauyi na isar da sako mai tsarki.
Gudanar da zaman makokin tunawa da ranar wafatin manzon Allah (SAW) a jahar California ta kasar Amurka, wanda cibiyar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke jahar za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa na nuni ne da ci gaban da musulmi suke samu wajen gudanar da harkokinsu na addini a kasar.
740674