IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani Ta Mata A Kasar Libya

16:24 - February 03, 2011
Lambar Labari: 2074683
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Libya, wadda aka yi wa taken wa’atasimu, da ke gudana yanzu haka yankin Tajura na birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran oqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arab online an habarta cewa, an fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Libya, wadda aka yi wa taken wa’atasimu, da ke gudana yanzu haka yankin Tajura na birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libya.
Babbar cibiyar kula da ayyukan addini da kuma harkokin zakka da zamantakewar jama’a ta birnin Tripoli ita ce ta dauki nauyin shirayawa da gudanar da wannan gasar hardar kur’ani mai tsarki a birnin, wadda ke samun halartar mahardata kimanin dari uku da hamsin350 dukkansu daga birnin, inda suke karawa da juna.
A daidai lokacin da aka fara gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Libya, wadda aka yi wa taken wa’atasimu, da ke gudana yanzu haka yankin Tajura na birnin Tripoli fadar mulkin kasar, a gefe guda kuma an fara gudanar da karatun kur’ani da ta kebanci maza kawai.
740322



captcha