IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani Ta Mata A Kasar Qatar

16:38 - February 03, 2011
Lambar Labari: 2074686
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci mata a yankin Al-ma’amura da ke cikin birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar mahardata mata daga sassan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-shrq an bayyana cewa, An fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da ta kebanci mata a yankin Al-ma’amura da ke cikin birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar mahardata mata daga sassan kasar ta Qatar.
Bayanin ya ci gaba da cewa baya ga gasar hardar kur’ani, a bangare guda kuma an bude wani shiri na bayar da horo ga masu bukatar hardar kur’ani mai tsarki, shirin da zai kwashe tsawon watanni shida ana gudanar da shi, inda yanzu haka aka samu daruruwan mata da suka yi rijista kuma suka shiga cikin shirin.
Daga cikin sharuddan shiga cikin wannan shiri dai dole ne yarinya ta kammala karatun sakandare, tare da kawo takardun shedar kammala karatun, inda bayan kammala samun horon za abata takardar kamalla samun horon hardar kur’ani mai tsarki mai inganci.
740246
captcha