IQNA

Taron Makokin Rasuwar Allamah Ayatollah Muhmamad Ali Al-Uamari A Bahrain

17:32 - February 05, 2011
Lambar Labari: 2075657
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taron makoki da juyayin rasuwar Allamah ayatollah Muhammad Ali Al-Umari a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, babban malamin addinin musulunci da Allah ya yi wa rasuwa a birnin Madina.
Kamfanin dilalncin labarann iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taron makoki da juyayin rasuwar Allamah ayatollah Muhammad Ali Al-Umari a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, babban malamin addinin musulunci da Allah ya yi wa rasuwa a birnin Madina mai alfarma.
Wannan zaman taro malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar Bahrain ne suka shirya gudanar da shi aHusainiyar Snas da ke birnin na Manama, taron zai samu halartar manyan malamai da kuma masana gami da mutanen gari daga sassa daban-daban na kasar.
Malaman musulunci za su gudanar da wani zaman taron makoki da juyayin rasuwar Allamah ayatollah Muhammad Ali Al-Umari a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, babban malamin addinin musulunci da Allah ya yi wa rasuwa kuma aka rufe shi a Baki’a.
741434




captcha