IQNA

An Kawo karshen Gasar Hardar Kur’ani Da Tajwidi Ta Kasa A Mali

17:33 - February 05, 2011
Lambar Labari: 2075659
Bangaren kasa da kasa, An kawo karshen gasar hardar kur’ani mai tsarki da kuma tajwidi ta kasa a kasar Mali, wadda aka gudanar a birnin Bamako fadar mulkin kasar tare da halartar mahardata daga sassa na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alfariq an bayyana cewa, an kawo karshen gasar hardar kur’ani mai tsarki da kuma tajwidi ta kasa a kasar Mali, wadda aka gudanar a birnin Bamako fadar mulkin kasar tare da halartar mahardata daga sassa na kasar, wadda aka gudanar a karo na farko.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartar mahardata kur’ani 57 da suka hada da maza da kuma mata, wadanda suka kara da juna, an fitar da dukkanin wadanda suka samu matsayi a cikin gasar, kama daga matsayi na farko na biyu da kuma na uku a dukkanin bangarorin gasar.
An kawo karshen gasar hardar kur’ani mai tsarki da kuma tajwidi ta kasa a kasar Mali, wadda aka gudanar a birnin Bamako fadar mulkin kasar tare da halartar mahardata daga sassa na kasar.
741389

captcha