IQNA

An Buga Kwafin Kur’ani Da Tarjama A Cikin Harshen Hausa A Sudan

17:31 - February 05, 2011
Lambar Labari: 2075660
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen Hausa a kasar Sudan, wanda cibiyar Darul Mushaf da ke birnin Khartum fadar mulkin kasar ta dauki nauyin bugawa da yadawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, an buga tare da yada wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen Hausa a kasar Sudan, wanda cibiyar Darul Mushaf da ke birnin Khartum fadar mulkin kasar ta dauki nauyin bugawa da yadawa a kasar domin amfanin masu magana da harshen Hausa da suke kasar.
Bayanin ya ci gaba da cibiyar ta gudanar da wannan aikin ne tare da hadin gwiwa da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ISESCO, wannan dai na daga cikin irin ayyukan da kungiyar take gudanarwa a kasashen Afirka, kafin nan an tarjama wasu kwafi-kwafin kur’ani a cikin harshen sawahili.
An buga tare da yada wani kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harsunan Wolof da ma wasu harsunan Afirka da suka hada da Hausa a kasar Sudan, wanda cibiyar Darul Mushaf da ke birnin Khartum fadar mulkin kasar ta dauki nauyin bugawa da yadawa.
741291



captcha