Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar shirye-shiryen gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka yi wa taken itqan a birnin Khuruj na kasar Saudiya, da nufin karfafa gwiwar matasa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan kur’ani ta fuskancin harda da kuma tadabburin ayoyinsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar iqtisadiyya an habarta cewa, an fara gudanar shirye-shiryen gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka yi wa taken itqan a birnin Khuruj na kasar Saudiya, da nufin karfafa gwiwar matasa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan kur’ani ta fuskancin harda da kuma tadabburin ayoyinsa masu tsarki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za ta kebanci matasa ne kawai wadanda suke yin harda da kuma karatun kur’ani, kuma cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta ma’aikatar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar saudiyya ce ta dauki nauyin shiryawa da gudanar da wannan gasa.
An fara gudanar shirye-shiryen gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka yi wa taken itqan a birnin Khuruj na kasar Saudiya, da nufin karfafa gwiwar matasa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan kur’ani ta fuskancin harda da kuma tadabburin ayoyinsa.
741382