Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin zalitan na kasar Libya domin kalu balanatar masu akidar kyamar addinin muslunci musamman a cikin kasashen yammacin turai, da suke nuna matukar gaba ga addinin Musulunci da ma dukkanin musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa kawancen jami'oin kasashen musulmi ne tare da hadin gwiwa da kungiyar bunkasa harkokin al'du da ilmomin addinin muslunci ta duniya ISESCO suka dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan zaman taro.
Rahoton za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin zalitan na kasar Libya domin kalu balanatar masu akidar kyamar addinin muslunci musamman a cikin kasashen yammacin turai da nufin tsokanar mabiya addinin Musulunci.
741883