Bangaren kasa da kasa, an afara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan koyon karatun kur’ani mai tsarki a cibiyar nazarin ilmomin addinin musulunci da ke birnin Sydney fadar mulkin kasar Australia.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muslim village an bayyana cewa, an riga an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan koyon karatun kur’ani mai tsarki a cibiyar nazarin ilmomin addinin musulunci da ke birnin Sydney fadar mulkin kasar Australia, da nufin kara karfafa gwiwar musulmi da suke bukatar koyon karatun littafi mai tsarki.
Wannan shiri dai yana daga cikin shirye-shiryen da wannan cibiya ta saba gudanarwa a kowace shekara, amma a wannan shekara shirin zai banbanta da sauran wadanda suka gabace shi, domin kuwa za a koyar da karatun kur’ani da kuma ilimin sanin ka’idar karatun kur’ani.
Bayanin ya kara da cewa afara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan koyon karatun kur’ani mai tsarki a cibiyar nazarin ilmomin addinin musulunci da ke birnin Sydney fadar mulkin kasar Australia, a babban ginin cibiyar.
740735