IQNA

An Fitar Da Wani Littafi Kan Yunkurin Imam Hussain (AS) A Karbala

10:45 - February 06, 2011
Lambar Labari: 2075967
Bangaren kasa da kasa, An fitar da wani littafi da aka buga dake yin magana kan yunkurin Imam Hussain (AS) wanda cibiyar kula da ayyukan hubbaren Imam da ke birnin karbala ta dauki nauyin rubutawa da kuma bugawa a cikin harshen farisanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun an bayyana cewa, An fitar da wani littafi da aka buga dake yin magana kan yunkurin Imam Hussain (AS) wanda cibiyar kula da ayyukan hubbaren Imam da ke birnin karbala ta dauki nauyin rubutawa da kuma bugawa a cikin harshen farisanci domin amfanin masu fahimtar harshen.

Littafin dai yana dauke da bayanai da suka dangaci matsayin yunkurin Imam Hussain (AS) a ranar Ashura, da yadda hakan ya zama wata babbar garkuwa ga addinin muslunci na asali da manzon Allah (SAW) ya zo da shi, wanda kuma hakika gwagwarmayar Imam Hussain ita ce babban sirrin wanzuwarsa.

Fitar da littafin da aka buga dake yin magana kan yunkurin Imam Hussain (AS) wanda cibiyar kula da ayyukan hubbaren Imam da ke birnin karbala ta dauki nauyin rubutawa da kuma bugawa a cikin harshen farisanci, zai taimaka ma masu fahimtar harshen domin kara sanin matsayin Imam Hussai (AS).


741787






captcha