Bangaren kasa da kasa, An gudanar da tarukan goma na karashen watan safar a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, da suka hada da arba'in din Imam Hssain (AS) wafatin manzon Allah (SAW) shahadar Imam Hassan Almujataba (AS) shahadar Imam Ali bin Musa Reza (AS)
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic centre an bayyan acewa, an gudanar da tarukan goma na karashen watan safar a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, da suka hada da arba'in din Imam Hssain (AS) wafatin manzon Allah (SAW) shahadar Imam Hassan Almujataba (AS) shahadar Imam Ali bin Musa Reza (AS) wanda cibiyar Musulunci ta birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa.
A lokacin gudanar da tarukan an gabatar da jawabai ga mahalarta taron, dangane da matsayin dukkanin bayin Allah da aka ambaci rashinsu da al'ummar musulmi ta yi, kama daga manzon tsira (SAW) da kuma sauna limaman ahlul bait uku (AS)
A lokacin gudanar da zaman taron musulmi da suka hada sunna da kuma mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah (SAW) duk sun halarci babban dakin gudanar da taruka na cibiyar.
Akwai dubban mabiya mazhabar iyalan gidan gidan manzon Allah da suke zaune a birnin London da suke halaratr tarukan addini da wannan cibiya kan daukin nauyin shirywa .
741770